An zargi Kurdawan Siriya da sakin 'yan IS
October 14, 2019Turkiyya ta zargi Kurdawan arewacin Siriya da sakin mambobin kungiyar IS da suke tsare da su da gangan da nufin sake jefa yankin a cikin bala'i a daidai loakcin da sojojin Turkiyya suka kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawan yankin.
Wata majiya ta hukumomin kasar ta Turkiyya da ba ta so a bayyana sunanta ba ta ce mambobin kungiyar na IS sun tsere ne daga gidan yari na birnin Tal Abyad, birnin da sojojin Turkiyyar suka kwace daga hannun mayakan Kurdawan na Kungiyar YPG a ranar jiya Lahadi.
Ya kara da cewa lokacin da sojojin Turkiyya suka isa gidan kason birnin na Tal Abyad sun tarar babu kofa daya da aka bankare, wanda ke nufin cewa bude wa mambobin kungiyar ta IS da ke tsare kofofin ne aka yi suka fice kawai. Sojojin Turkiyyar sun kuma sanar da tarar da zanen hoton Abdullah Öcalan shugaban jam'iyyar PKK wanda hukumomin Ankara ke tsare da shi.