1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta daina kasuwanci da kamfanin Turkiyya

Abdul-raheem Hassan
September 22, 2020

Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadarai da matakin kungiyar Tarayyar Turai na sa takunkumin karya tattalin arziki kan wani kamfaninta da ake zargi da saba yarjejeniyar makamai a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3ip7E
Türkei Präsident Erdogan
Hoto: picture-alliance/AA/M. Kamaci

Ministocin kungiyar Tarayyar Turai sun amince da katse huldar kasuwanci da kamfanonin uku na kasashen Turkiyya da Kazakhstan da Jordan da aka samu da safarar makamai tun watan Junin 2020.

Sai dai ana ganin sanya wa kamfanin Turkiyya takunkumi zai iya tada kwantaccen rikici tsakanin Ankara da kasashen EU a kan arzikin mai da makamashin iskar Gas da ake takaddama a gabashin Tekun Bahar Rum.