Turkiyya ta kori wata 'yar Jaridar Holland
January 17, 2019Talla
Turkiyya ta sanar da korar 'yar jaridar kasar Holland Ans Boersma daga kasarta bayan ta sami bayanai cewa tana da alaka da kungiyar 'yan ta'adda.
Jaridar da ta ke yiwa aiki Het Financieele Dagblad ta soki matakin da cewa ya keta 'yancin 'yan jarida.
Rundunar yan sandan Holland ta ki cewa uffan akan batun.
Sai dai fadar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da sanarwar cewa hukumomin Turkiyya sun sami bayanan sirri daga 'yan sandan Holland game da alakar ta da wata kungiyar ta'adda sannan sun nemi bayanai game shige da ficenta a cikin Turkiyya.