Turkiyya ta gargadi Turai kan barazanar hare-hare
January 18, 2020Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya, ya gargadi kasashen Turai kan yiwuwar su fuskanci hare-hare daga kungiyoyin ta'adda, muddin aka kawo karshen gwamnatin Fayez al-Sarraj da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a Libiya.
A wata makala da Turkiyyar ta wallafa a yau Asabar da ake jajibirin taron sasanta rikicin Libiya a birnin Berlin, Shugaba Erdogan ya ce idan har kungiyar Tarayyar Turai ta ki mara wa gwamnatin ta Libiya baya, to kuwa ta saba wa da'awar da take yi ta mutunta dimukuradiyya da kare hakkin dan Adam.
A farkon wannan makon ne dai Turkiyya da Rasha suka shirya tattaunawar neman tsagaita buda wuta da ak yi a birnin Mosko, sai dai an tashi ne ba tare da nasara ba, sakamakon ficewar da madugun yakin Libiya Khalifa Haftar ya yi ba tare da sanya hannu ba.