Turai tana kyama da wariya ga bakar fata saboda Ebola
October 17, 2014Jaridar Tageszeitung ta duba cutar Ebola, to sai dai ta wata fuskar dabam. Tace yayin da yawan masu fama da cutar ke karuwa, ba ma a nahiyar Afirka kadai ba, tsoronta kuma yana kara bunkasa. Abin da ya zama sakamakon hakan kuwa, musamman a nan Turai, shine nuna kyama da wariya ga duk wani bakar fata mazaunin wannan nahiya. Jaridar Tageszeitung ta bada labarin wani dan wasan kwallon kafa bakar fata, wanda daga shigarsa filin wasa, yan kallo suka rika kiran Ebola, Ebola. Hakan injita, yana nufin ga Turawa, yanzu duk wani bakar fata mutum ne mai dauke da vcutar Ebola. Sai dai kuma ba ga yan kasa kawai ba, har ma yan siyasa da jami'an tsaro, sun fara nuna alamun kyama ga 'yan kasashen Afirka gaba daya dake zaune a Turai. Wannan kyama bata tsaya kan wata kasa ta Turai guda daya kawai ba. A Italiya, har ma 'yan siyasa suna kira ga dakatarda taimako ga 'yan gudun hijira daga kasashen Afirka, saboda tsoron ko suna dauke da cutar ta Ebola da zasu iya shigar da ita kasashen na Turai.
Bisa dacewa da wannan kyama ga bakar fata saboda Ebola, jaridar Berliner Zeitung tace cutar Ebola ta kama hanyar yin balaguro zuwa ketare daga makwancinta a Afirka ta yamma. A Turai ana kara nuna damuwa game da samun yaduwar cutar, inda ma ministocin kiwon lafiya na kasashen suka nemi a kara tsananta matakan bincike a tashoshin jiragen saman kasashen Afirka ta yamma. A wannan mako, sau biyu ana samun alamu na shigowar cutar nahiyar Turai, misali a Denmark inda aka yi gwajin wani ma'aikacin taimkon raya kasa da ya taso daga Afirka ta yamma, yayin da a Spain, jami'an kiwon lafiya suka tsare wani jirgin sama da ya fito daga Paris, bayan da wani fasinja dan Najeriya, ya nuna alamun zazzabi mai tsanani. Jaridar Berliner Zeitung tace abin da Turai take ganinsa nesa da ita, yanzu ya matso kusa. Nahiyar ta dade tana zura idanu tare da kyale kasashen Afika ta yama uku, wato Saliyo, Guinea da Liberiya suna gwamarmayar yadda zasu shawo kan cutar, amma yanzu da ta fara tattaki zuwa garesu, halayensu ga cutar sun banbanta.
Jaridar Süddeutsche Zeitung ta tabo batun zaben shugaban kasa ne a Mozambik a wannan mako, inda tace ba kamar yadda aka saba a kasar ba, a wannan karo duka 'yan siyasar da abin ya shafa sun nuna alamar kiyaye tsari na dimokradiya a zaben na bana. Dan takarar dake kan gaba a zaben na shugaban kasa, shine wakilin jam'iyyar dake mulki ta FRELIMO, Filipe Nyusi, yayin da dan takara na jam'iyyar adawa, kuma tsohuwra kungiyar sari ka noke, RENAMO, wato Alfonso Dlakama yake bin bayansa. Filipe Nyusi shine ake sa ran zai gaji mukamin na shugaban kasa daga mai barin gado, Armanfdo Guebuza, wanda tsarin mulkin Mozambik bai bashi damar wa'adi fiye da biyu ba. Zaben na bana, ya biyo bayn yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka sanya hannu kanta ne yan watanni kalilan da suka wuce, wadda ta kawo karshen yakin basasa na tsaron fie da shekaru 15. Jaridar Süeddeutsche Zeitung tace ganin shugaba Armando Guebuza ya ajiye mukaminsa bayan wa'adi biyu, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar, wata babbar alama ce ta ci gaba a kasar da tun da ta sami mukin kanta daga Portugal a shekara ta 1975, take karkashin mulkin jam'iyar siyasa daya, wato jam'iyar Frelimo.