1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya ta bayyana ceto bakin haure a kan teku

Suleiman Babayo ATB
November 26, 2021

Mahukunta sun ceto bakin haure kimanin 500 daga kan teku masu neman shiga kasashen Turai. Hukumomin Tunisiya sun ce mutanen da aka ceto suna yunkurin shiga Turai daga Libiya.

https://p.dw.com/p/43XPM
Rettungsschiffe Sea-Watch 3 und Ocean Viking retten 394 Migranten im Mittelmeer
Hoto: Darrin Zammit Lupi/REUTERS

Mahukuntan Tunisiya sun bayyana ceto bakin haure kimanin 500 da jirgin ruwansu ya lalace a kokarin shiga kasashen Turai. A wannan Jumma'a masu gadin bakar ruwan kasar da ke yankin arewacin Afirka suka ceto bakin haure galibi 'yan kasashen nahiyar Asiya da Laraba da 'yan Afirka na Kudu da Sahara. Akwai mutanen da aka ceto akwai mata da yara.

Shi dai wannan jirgin ruwa da mahukuntan Tunisiya suka ceto ya fito ne daga kasar Libiya, kamar yadda hukumomin suka tabbatar.