1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da tashin hankalin kyamar baki a Rostock

August 21, 2012

A watan Agusta na shekara ta 1992, aka sami barkewar tashin hankali a garin na jihar Mecklenburg Pommerania da ya zama alamar kyamar baki a nan Jamus

https://p.dw.com/p/15ttB
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan lokaci yan sanda da yan siyasa sun kasa daukar wani mataki na kawo karshen tashin hankalin, kuma tun daga lokacin duniya gaba daya ta maida Rostock ya zama wata alama ta rashin rashin kaunar baki a Jamus.

Duniya gaba daya ta shaidar da hotunan da akai ta nunawa na gidajen da akai ta kunna masu wuta a yankin Lichtenhagen na Rostock a watan Agusta na shekara ta 1992, yayin da yan Nazi da masu kyamar baki sukai ta kuwwar adawa da baki da yan gudun hijira da jifa da duwatsu da jefa bama-baman wuta a gidajen jama'a, mafi yawan su masu neman mafakar siyasa da aka tsugunar dasu a wannan yanki. Sauran mazauna garin da suka taru, sun rika yiwa yan Nazin tafi suna yi masu kirari.

Deutschland Rechtsradikale Gewalt gegen Ausländer in Rostock-Lichtenhagen 1992
Yan sanda da masu kyamar baki a RostockHoto: picture-alliance/dpa

Wakilin birnin Rostock game da zaman baki, Wolfgang Richter, shi kansa yana daya daga cikin gidajen a lokacin da tashin hankalin ya barke.

Yace daga cikin gidan idan muka leka waje, sai mu hangi yadda dubban mutane suka kewaye mu da duwatsu suna jefa bama-baman wuta cikin wannan gida, kamar yadda yadda aka rika yi a a daren da yan Nazi suka rika farautar Yahudawa. Tashin hankalin yayi tsanani yadda babu wani tunani na abin dake gudana, inda masu kai mana hari babu abin da ya dame su, ko mutane 100 ne a cikin gidan, ko kuma su damu cewar gaba dayan su suna iya mutuwa idan wuta ta cinye gidan gaba daya.

To sai dai wani abin mamaki shine babu wanda ko ya sami rauni daga aiyukan na masu kyamar baki, ko da shike sun yi kwanaki biyu suna mamaye da gidan na yan gudun hijira masu neman mafakar siyasa, kafin yan siyasa su dauki matakin kwashe yan gudun hijiran cikin manyan motoci domin kare lafiyar su.

Masu kyamar bakin daga wannan lokaci suka maida fushin su a wannan gida ga yan Vietnam da suka rage da kuma kan yan sanda. Da farko yan sanda 30 aka tura domin dakatar da yan Nazin kimanin 300 amma koda shike daga baya an kara yawansu, amma ba'a basu isassun kayan aiki da suke bukata ba. A daura da haka, yan banga da yan Nazi suka rika sauka a garin daga ko ina a yankin, inda a karshe yawansu ya kai kimanin 1000.

A wannan lokaci kamar dai a yanzu, an rika tambayar: shin yaya aka yi har aka kai ga yadda abin ya baci haka. Prof Hajo Funke, masani a fannin matsalar kyamar baki a jami'ar Berlin yace wannan mummunan tashin hankali ya samu ne saboda kawar da aka samu a fannoni da dama.

Abin da yafi muhimmanci kamary adda nake gani, shine yadda birnin Rostock da jihar Mecklenburg Pommerania ko taraiya suka kyale tashin hankalin ya tsananta, kuma suka kasa daukar wani mataki na shawo kansa. Saboda haka wannan ana iya cewa ya smau ne saboda rashin karfin zuciyar yan siyasa na shawo kan labarin, wanda ake iya cewar hukumomi ne suka kyale masu kyamar bakin suka shiga farautar yan gudun hijira.

Deutschland Rechtsradikale Gewalt gegen Ausländer in Rostock-Lichtenhagen 1992
Yan gudun hijira sun ga ta-kansu a birnin RostockHoto: picture-alliance/dpa

Daga karshe dai an yanke hukunci ga wadanda suka kaiwa gidajen na yankin Lichtenhagen hari kimanin 44 dauri na misalin shekaru uku a gidan kaso, yayin da ministan cikin gida na jihar, da magajin garin Rostock tilas suka yi murabus. Ya zuwa yanzu, ba'a gano wanda yake da alhakin rudamin da aka shiga game da dakatarda tashin hankalin a birnin Rostock ba. Duk da haka, wani dan Vietnam mai suna Thinh Do, da ya kasance a gidan, lokacin da yan Nazin suka kai masa hari, yayi imanin cewar birnin Rostock ya koyi darasi, shekaru 10 bayan wnanan tashin hankali.

Yace ban yi tsammanin irin haka zai sake faruwa a Rostock ba, saboda karamar hukumar birnin da yan sanda sun fahimci irin yadda halin zama yake a yankin Lichtenhagen na Rostock.

Shima masani kan batun kyamar baki, Hajo Fuke yana da ra'ayin cewar farautar baki da yan Nazi suka yi shekaru 10 da suka wuce a birnin da yadda ya dauki hankalin kafopfin yada labarai, ya sanya yan sanda sun kasance cikin wani sabon shiri na ko-ta-kwana domin hana sake aukuwar hakan nan gaba.

Mawallafi: Fuchs/Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman