Tsohon shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor ya gurfana a gaban kotu a kasar Saliyo
April 3, 2006Tsohon shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor wanda ya gurfana yau a gaban kotun kasa da kasa dake Saliyo ya ƙi amsa tuhumar da ake masa ta aikata laifukan yaƙi da kuma cin zarafin alúma. Da farko Charles Taylor ya baiyana cewa ba zai ce uffan ba, domin bai amince da halascin kotun ba ta yi masa shariá, daga bisani ya shaidawa mai shariár Justice Richard Lussick cewa bai aikata laifin komai ba. Charles Taylor yace babu yadda zaá ce shi ya aikata taásar da suka faru a lokacin yaƙin basasar kasar Saliyo. Kotun ta karbi bayanan da yayi a matsayin madogara ta shariá. Jamaá da dama na fatan shariár sa, za ta sanya shugabanin ƙasashen Afrika shiga cikin taitayin su, cewa ba su fi karfin shariá ba. A halin da ake ciki kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na nazarin bukatar sauya matsugunin kotun daga Saliyo zuwa birnin Hague a kasar Netherlands saboda matakan tsaro.