1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta kadu da labarin rasuwar Shinzo Abe

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
July 8, 2022

Shinzo Abe da ke zama tsohon firaministan Japan ya rasu sakamakon mummunan raunin da ya samu biyo bayan harbinsa da wani dan bindiga ya yi.

https://p.dw.com/p/4Dq88
Japans Ex-Regierungschef Shinzō Abe nach Attentat gestorben
Hoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Kasashen duniya na cigaba da nuna kaduwa game da harin da aka kai wa tsohon firaministan Japan Shinzo Abe a yayin da yake tsaka da gangamin siyasa.

Babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken a yayin da yake ganawa da 'yan jarida a taron ministocin harkokin wajen G20 na birnin Bali ya ce Amirka ta kadu da jin labarin rasuwar Firaminista Abe sakamakon mummunan raunin da ya samu biyo bayan harbinsa da wani dan bindiga ya yi. 

Da sanyin safiyar wannan Jumm'ar ce aka garzaya da tsohon firaminitan na Japan zuwa wani asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, sakamakon buda wutar da wani dan bindiga ya yi masa lokacin da yake jagorantar wani gangamin siyasa.

Binciken farko dai ya yi nuni da cewa maharin wani tsohon jami'in tsaro ne da ya bar aiki a shekarar 2005