Atal Bihari Vajpayee tsohon firaministan Indiya ya rasu
August 16, 2018Talla
A dazu-dazun nan ne aka sanar da rasuwar tsohon firaministan kasar Indiya Atal Bihari Vajpayee, mai shekar 93 da haihuwa, bayan da ya shiga cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya a birnin New Delhi. Firaminisrtan kasar ta Indiya ne dai na yanzu Narendra Modi, ya sanar da labarin mutuwar.
Vijapayee, ya jagorancin kasar ta Indiya ne har sau uku inda na farko a shekara ta 1996, sai na biyu a tsakanin shekara ta 1998 zuwa 1999 sannan wa'adi na uku ya yi shi ne daga shekara ta 1999 zuwa 2004.
Marigayin ya jima yana fama da rashin lafiya a cewar likitocinsa inda watanni biyu da suka gabata ma an kwantar da shi bayan da ya yi fama da matsalar koda da kuma jiyon kirji.