Tsawa ta halaka manoma a Indiya
July 28, 2022Talla
Rahotanni daga Indiya, na cewa tsawa ta kashe mutane bakwai yawancinsu manoma a wani kauye da ke arewacin jihar Uttar Pradesh, 'yan sanda sun ce tsautsayin ya ritsa da manoman ne a lokacin da suke samun mafaka daga saukar ruwan sama a karkashin wata bishiya a ranar Talata.
Yanzu haka dai hukumomi jihar sun tabbatar da adadin mutane 49 tsawa ta yi ajalinsu a cikin mako guda, wannan ya sa gwamnatin daukar sabbin matakai na nunawa mutane dabarun kare kansu daga tsawa.