1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin kudin Euro na bukatar gyara

June 5, 2012

Rikicin kudi da na bankuna a Turai ya sanya shugabanni a nahiyar su fara tunanin yadda za'a ceto kudin bai-daya dake tsakanin su

https://p.dw.com/p/158Fw
Hoto: picture alliance/dpa

Wata jarida ta nan Jamus mai suna Welt am Sonntag ta gabatar da rahoton cewar kasashen Turai suna wani shiri cikin sirri, a yunkurin farfado da kudin nahiyar wato Euro. Jaridar tace wadanda suke aiki kan wannan shiri na sirri kuwa sune shugaban kungiyar hadin kan Turai Herman Van Rompuy da shugaban hukumar kungiyar, Jose Manuel Barosso da kuma shugaban majalisar rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro, Jean-Claude Juncker tare da shugaban babban bankin Turai, Mario Draghi.

To sai dai wannan shiri nasu ba wani na sirri bane a zahiri, domin kuwa tun a lokacin taron kolin da shugabanin kungiyar hadin kan Turai suka yi ranar 23 ga watan Mayu, aka baiwa jami'an izinin aiki kan wani tsari da zasu gabatarwa taron koli na gaba, a game da yadda za'a shawo kan rikin kudi da kungiyar take fama dashi, kowa ya huta. Sai dai kuma tun bayan da masanan suka fara aiki kan matakan nasu, rikicin kudin na Turai ya kara tsananta. Maganar a yanzu, ba ita ce ko kasar Girka zata ci gaba da zama a hadin kan kudin Euro ba, amma abin dake kawo damuwa shine ko Spain ita ma zata iya ceto bankunan kasar dake fama da dimbin bashi a kansu. Tun a makon jiya, shugaban hukumar kungiyar hadinkan Turai, Jose Manuel Barosso dake tsokaci da Spain, ya kawo shawarar samar da wata hukuma ta bai-daya da zata rika kula da aiyukan bankuna da hana su cin bashin da yafi karfin su.

Ko da shike a wannan lokaci Barosso bai yi karin bayani game da abin da yake nufi ba, amma ranar Litinin aka sami karin haske. Kwamishinan harkokin kudi na kungiyar, Olli Rehn, bayan da ya gana da sabon ministan kudi na Faransa, Pierre Moscovici, yace yana da muhimanci a sami wani tsari inda asusun nan na ceto da kasashen Turai suka kafa, wato EFSF Da ESM, zasu rika taimakawa bankuna kai tsaye da zaran an ga alamaun sun fara rauni. Ya zuwa yanzu wadannan asusu kasashe kadai suke iya baiwa taimako amma ba bankuna ba, abin da Jamus inda so samu ne, tafi son kada a canza ga wannan tsari. A daura da haka, ministan kudin na Faransa yace kasar sa tana kaunar ganin an sami tsarin da bankunan Turai zasu kasance karkashin hukuma daya. Yace yana ma son ganin wnanan bukata an shigar da ita a jerin abubuwan da za'a tattauna kansu a lokacin taron koli na gaba a karshen watan Yuni.

Merkel empfängt Draghi
Shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel da kwamishinan kudi na EU, Mario DraghiHoto: picture alliance/dpa

Duk da haka, a lokacin ganawar da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel tayi da shugaban hukumar kungiyar hadin kan Turai, Manuel Barosso a Berlin, ta nuna cewar Jamus tana iya yin sassauci.Tsarin da aka gabatar da hadin kan al'amuran haraji, mataki ne na farko, wanda kuma shi kadai ba zai wadatar ba.

Saboda haka ne zai kasance wajibi ne mu tattauna mu ga yadda za'a iya maida bankunan na Turai karkashin hukumar kula ta hadin gwiwa, yadda bukatun kasa da kasa ba zasu rika taka wata muhimiyar rawa a aiyukan su ba.

Merkel ta maida martani ne kan ga wani jawabi da shugaban babban bankin Turai, Mario Draghi yayi, gaban kwamitin harkokin kudi na majalisar dokokin kasashen Turai, inda yace ba zai yiwu a ci gaba da kiyaye tsarin dake aiki yanzu tattare da kudin Euro ba.

Tsarin da kudin Euro yake aiki karkashin sa, kamar yadda muka gabatar shekaru 10 da suka wuce, kuma muka yi tsammanin zai dore har abada, yanzu mun lura da cerwar ba zai kai ko ina ba, sai fa idan an dauki karin matakai na yi masa kwaskwarima.

WDR Europaforum 2012 Brüssel Belgien
Shugaban majalisar Kungiyar Hadin kan Turai, Herman Van RompuyHoto: dapd

Wannan jawabi da ba'a maida hankali kansa a makon jiya ba, a yanzu sannu a hankali an fara gane muhimmancin sa. A takaice, kudin Euro ba zai ci gaba a tsarin da aka shi yanzu ba.

A halin yanzu dai manyan shugabannin siyasa na nahiyar Turai sun kai ga fahimtar cewar daukar yan kananan matakai da basu taka kara sun karya ba, ba zasu kai ga nasarar ceto hadin kan na kudin Euro ba. Sai dai kuma ko da shike wasu daga cikin su suna bukatarf daujkar manyan matakai masu tsanani cikin gaggawa, amma kasashen da mafi yawan nauyin hakan zai tattara a kansu, kamar misali Jamus, suna bukatar taka tsan-tsan kan al'amarin.

Mawallafi: Hasselbach/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman