Tsamin dangantaka tsakanin Merkel da Trump
May 31, 2017Dangantakar shugabannin biyu ta kara lalacewa ne a taron Kungiyar G7 da ya gabata, inda Shugaba Trump ya zargi Jamus da ha'intar Amirka a cikin huldar kasuwancin kasashen biyu da kuma ke haddasa wa Amirkar babbar Asara. Lamarin da ya sa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fakaice ke ta yawaita suka da kakkausan lafazi ga manufofin siyasar Donald Trump din duk da yake cewa ba ta ambato sunansa a bayyane ba.
Angela Merkel wacce ta yi kira ga kasashen Turai da su kara hada kansu, ta bayyana wa 'yan kasar ta Jamus cewa zamani irin wanda suke dogaro da Amirka ba tare da wani shakku ba ya shude a yanzu. Shi ma dai daga nashi bangare Shugaba Trump ya mayar da martani a shafinsa na Tweeter inda ya zargi Jamus da kin zuba kudaden da ya kamata wa rundunar tsaron kasa da kasa ta NATO, lamarin da ya ce Amirka ba zata lamunta da shi ba kuma za ta dauki matakin kawo sauyi a kai.