Tsamin dangantaka tsakanin Holland da Turkiya
March 12, 2017Talla
Mahukuntan Netherlands din dai sun hana ministan harkokin wajen Turkiyya sauka a birnin Rotterdam a jiya Asabar, a ci gaba da nuna adawa da yunkurin neman goyon bayan Turkawa da ke zaune a ketare, kan tsawaita wa'adin mulkin shugaban Tayyip Recep Erdogan. Murat Saglam na daya daga cikin Turkawa masu gangamin...
" Me zan iya cewa? Wannan abun kunya ne a bangaren Turai. Babban abun kunya. Wannan lokaci ne da aka yi wa demokradiyya karan tsaye. Bai dace a yi wa wani ministan Turkiyya ko kuma na wata kasa irin wannan cin fuska ba".
Ministar kula da iyali ta Turkiyya Fatma Betul Sayan Kaya da ta yi kokarin ganawa da masu gangamin goyon baya ga shugaba Erdogan a birnin Rotterdam a jiya da maraice, ta tsinci kanta a kan iyakar Jamus.