Rikice-rikice
Yarjejeniyar kawo karshen rikicin Libiya
September 26, 2018Talla
Gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta bayyana shirin tsagaita wuta domin kawo karshen fada da tsageru masu dauke da makamai kimanin watan guda ke nan a kudancin birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar, inda fiye da mutane 100 suka rasa rayukansu, sannan wasu fiye da 400 suka jikata.
Wata sanarwar ma'aikatar cikin gida ta ce wakilan bangarorin sun saka hannu kan yarjejeniyar a garin Tarhuna da ke kudu maso gabashin birnin na Tripoli. kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka tana tsunduma cikin yakin basasa tun shekara ta 2011 bayan kawo karshen gwamnatin Marigayi Shugaba Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.