Majalisar wakilan Amirka ta tsige Trump
January 14, 2021Talla
Wannan dai al'amari na tsige shugaban Amirkan da majalisar ta yi, ya dau hankal kasashen duniya, ko da shi ke ma hukunci ba shi da tasiri kai tsaye sai idan har majalisar dokoki ita ma ta kada kuri'a tsige shugaban. To amma da yake magana jim kadan bayan majalisar wakilan kasar ta sanar da tsige shi daga madafun iko, Trump ya ce babu wani wanda ya fi karfin doka a Amirka, yana mai ikirarin cewa masoyinsa na zahiri ba zai aikata irin wannan ba. Ya sha alwashin sai an hukunta duk mutanen da suka yi kutsen.