Trump ya soke fifikon cinikayya da Indiya
June 1, 2019Talla
Shugaba Donald Trump wanda ya sanar da hakan a ranar Juma'a yace matakin zai fara aiki daga ranar laraba mai zuwa.
Trump yace ya dauki matakin ne saboda Indiya bata gamsar da Amirka cewa za ta bada makamancin wannan dama ga Amirkar a kasuwanninta ba.
Tun fiye da shekaru 40 da suka wuce Amirka ta bada wannan dama ga wasu kasashe masu tasowa su shigar da wasu nau'in kayayyakinsu cikin Amirka ba tare da biyan haraji ba a wani mataki na taimakawa cigaban kasashen.
Gwamnatin Indiya ta baiyana matakin na Trump a matsayin wani babban abin takaici. Sai dai ta ce za ta cigaba da karfafa dangantakar tattalin arziki da Amirkar.