1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Touadéra ya tsaya takara a zaben Disamba

Mouhamadou Awal Balarabe
September 26, 2020

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya yi amfani da babban taron jam'iyyarsa ta MCU wajen bayyana aniyar tsayawa takara a zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga watan Disamba 2020.

https://p.dw.com/p/3j3Cd
Faustin Archange Touadera
Hoto: imago/Pacific Press Agency

Touadéra ya yi wannan shelar ne a gaban mambobin jam'iyyarsa ta MCU da suka hallara a zauren babban taro da suka shirya a Bangui babban birnin kasar. Wannan takarar dai ba ta zo da mamaki duk da cewa  kashi biyu cikin uku na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na karkashin ikon kungiyoyin ‘yan tawaye bayan da ta yi fama da yakin basasa na sama da shekaru bakwai.

Har yanzu dai ana tababa game da  yiwuwar gudanar da zaben na shugaban kasa cikin watanni uku masu zuwa, saboda ana fuskantar jinkiri wajen shirya shi musamman wajen rejistar masu kada kuri'a. Shi dai Faustin-Archange Touadéra da ya dare kan kujerar mulki a 2016 bai yi nasarar mayar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tsintsiya madaurinki daya ba, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin manyan kungiyoyin 'yan tawaye 14 da gwamnati. 

Tsohon shugaba Francois Bozizé na daga cikin wadanda suka tabbatar da takararsu a zaben na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.