1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi a Najeriya

July 18, 2024

An cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin na naira dubu 70 ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago.

https://p.dw.com/p/4iUDm
Zanga-zangar NLC a Najeriya
Zanga-zangar NLC a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun amince da sabon mafi karancin kudin albashi na naira dubu 70 kwatankwacin dalar Amurka 44 a kowane wata.

An cimma matsaya kan sabon albashin ne bayan tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da kuma gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

Karin bayani: Rikicin 'yan kodago da gwamnatin Najeriya

Wannan matsayar ta kawo karshen barazanar yaje-yajen aiki da kuma rashin tabbas a halin yanzu.

Kasar da ta fi ko wacce yawan al'umma a nahiyar Afirka na fama da tsadar rayuwa abinda wasu ke fargaba ka iya jefa ta cikin zanga-zanga kamar yadda ake gani a kasar Kenya da ke gabashin Afirka.

Karin bayani:Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da NLC kan yajin aiki

Manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya biyu NLC da TUC sun sha fadin cewa hauhawar farashin kayan masarufi da kuma tawayar darajar naira sakamakon manufofin shugaba Bola Tinubu sun jefa ma'aikata cikin mawuyacin hali.