SiyasaAfirka
Tattauna hanyoyin zabe a Libiya
October 26, 2020Talla
An bude taro da wakilai da dama daga kasar Libiya suke halarta domin tattauna harkokin siyasa ta hanyar taron bidiyo bisa matakan gudanar da zabuka bayan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin siyasa na kasar da ke yankin arewacin Afirka.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Libiya ya ce wannan tattaunawar za ta bude hanyar zama kai tsaye tsakanin bangarorin ranar 9 ga watan gobe na Nowamba a birnin Tunis fadar gwamnatin Tuniya.
Ranar Jumma'a da ta gabata bangarorin da ba sa ga maciji na juna a rikicin kasar Libiya suka amince da shirin tsagaita wuta, a kasar da ta tsunduma cikin rikicin siyasa tun shekara ta 2011.