1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali na karuwa a yankin Amhara

Mouhamadou Awal Balarabe
August 3, 2023

Gwamnatin Habasha ta bayyana cewar tashe-tashen hankula da ke wakana a yankin Amhara na haddasa damuwa a fannin tsaro, bayan wani artabu da aka yi tsakanin dakarun kasar da mayakan sa kai na wannan yanki.

https://p.dw.com/p/4Ujsr
Sojojin Habasha sun jima suna gwabzawa a yankin AmharaHoto: Seyoum Getu/DW

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mataimakin firaministan kasar Demeke Mekonnen ya ce Habasha na cikin yanayi maras kyau da zai iya kaita ga darewa gida biyu idan ba a tabbatar da zaman lafiya ba. Dama dai yawancin ofisoshin jakadanci na yammacin duniya sun shawarci 'yan kasarsu da su guji zuwa arewacin Habasha wanda ke fama da rashin kwanciyar hankali.

Yankin na Amhara ya fada cikin matsala tun lokacin da gwamnatin Habasha ta yunkura don tarwatsa 'yan gaggwarmaya da suka yi korafin cewar ana mayar da su saniyar ware. Dama dai yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen yaki a watan Nuwamba 2022 ba ta samu amincewar wani bangare na Kabilar Amhara da ke zama na biyu mafi girma a kasar ba.