1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarzuma gabanin zaben Zambiya

Usman Shehu UsmanAugust 10, 2016

An raunata mutane da dama biyo rikicin da ya barke kwanaki gabanin zaben shugaban kasar inda rikici ke ta karuwa tsakanin magoya bayan man'yan jam'iyyun siyasan kasar.

https://p.dw.com/p/1Jf5X
Wahlen in Sambia Unruhen Polizei
Hoto: AP

Tun a a ranar Litinin ne dai aka tsare wata motar safa, inda aka yi ta jifan fasinjojin da duwatsu, abinda ya jawo raunata mutane da dama, an kuma bada rahotonin samun barkewar tashin hankali a wasu sassan kasar. Neo Simutanyi, wani mai sharhi kan siyasar kasar ta Zambiya, ya fadawa DW cewa.

"Yanayin siyasar ya dau zafi, mutane na cike da tsoron barkewar babban tashin hankali. Kuma babu alamar lafawar tashin hankalin. Kwanaki uku zuwa biyu biyu gabanin zaben, ba abinda ake gani illa kara munin tarzuma tsakanin magoya bayan jam'iyyun.

Hukumar zabe da 'yan takaran shugaban kasan, duk sun yi Allah wadai da tarzumar da ta barke. 'Yan takara tara ne ke fafatawar a neman kujerar shugaban kasa, cikin zaben da zai gudana a karkashin sabbin dokokin zabe a kasar ta Zambiya.