Taron neman zaman lafiya
December 22, 2014A makon da ya gabata shugabannin kananan hukumomin na Jamhiriyar Afirka ta Tsakiya, suka hallara a Bangui babban birnin kasar, domin wata tattaunawa ta kwanaki uku, inda a yayin wannan tattaunawa, jagororin na kananan hukumomi, suka duba batutuwa masu dumbun yawa da yankunan na su suke fuskanta abin da ke zaman wani babban kalubale a gabansu.
Daya bayan daya dai shugabannin kananan hukumomin da suka hallara kowa ya yi bayani kan iri-irin halin da na shi yankin ke ciki, inda akasarin yankunan ke cikin mawuyacin halin rayuwa a wannan lokaci. Albert Nakombo shi ne Shugaban karamar hukumar Berberati, daya daga cikin kananan hukumomin da ake wa kallon cibiyar kasuwancin wannan kasa ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya yi wa DW karin haske kan halin da suke ciki da mahimmancin zaman lafiya wajen samun ci-gaba.
Rikicin ya janyo ficewar akasarin 'yan kasuwa daga kasar, musamman na kasashen ketare da ke ayyukansu na kasuwanci.
Wani babban kalubanan a wannan lokaci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya shi ne, ya yin da ake daf da shagulgulla na karshen shekara, har kawo yanzu ma'aikata a wannan kasa sun zuba idanu su ga ta inda albashi zai fito, duk da cewa yanayin bukukuwan karshen shekarar na tattare da tsadar rayuwa sannan ga batun rufe iyakar kasar da makwabciyarta ta Kamaru.