Nijar: Taron kungiyoyin farar hula ta yammacin Afirka
June 5, 2023A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fararen hula da sauran kwararru a fannin sanin dokokin shari'a da ma kimiyyar siyasa da suka fito daga sassa daban-daban na kasashen yammacin Afirka da Sahel, sun kammala zaman taronsu na kwanaki uku da Kungiyar Tournons la Page reshen Nijar ta shirya tare da taimakon uwar kungiyar ta kasa da kasa; domin duba yanayin da ake ciki a kasashe da dama na Afirka na hana 'yancin walwala ga kungiyoyin fararen hula da sauran masu adawa da gwamnatoci duk kuwa da cewa, ana cikin tsari na Dimukuradiyya.
Wannan babban zaman taro da ya gudana a birnin Yamai ya samu halartar kwararru kimanin 50 daga kasashe bakwai na yammacin Afirka da yankin Sahel, inda gabaki dayan mahalarta taron suka yi amannar cewa a cikin kasashe da dama na Afirka, akwai tarin matsaloli na rashin yarda tsakanin al'umma da gwamnatoci ta sabili da rashin mutunta tsarin da dimukuradiyya ta shimfida wanda ya bada damar walwala ga kungiyoyi ko da kuwa suna adawa da wasu matakai da gwamnatocin ke dauka.
Taron ya yi Allah-wadai da ci gaba da tsare 'yan kungiyoyin fararen hula mambobin kungiyar ta Tournons la page a kasashen Gabon da Togo da Burundi da kuma Abdoulaye Seidou na Nijar da dukanninsu ke ci gaba da zama a gidajen kurkuku ta sabili da ayyukansu na kare hakkin jama'a da 'yancin walwala, inda suka ce, ya kyautu gwamnatoci su sani wannan furjin mussa da suke yi ba wai zai ba su tsoro ba za su ci gaba da yin hannunka mai sanda da zaran magabaci ya saki hanya, tare da yin Allah-wadai da yadda ake hana 'yan adawa walwala kaman abin da ke wakana a kasar Senegal.
Da karshe dai wakillan kungiyoyin fararen hula da sauran kwararru da suka halarci wannan babban zaman taro na birnin Yamai, sun girka wata gamayyar kungiyar ta wadannan kasashe da za ta bi sau da kafa cikin gama karfi da karfe domin ganin al'umomi sun mori 'yancin da kundin tsarin mulki ya tanadar musu wanda mahakumta ke hanawa ta sabili da wasu dalillai na daban.