Taron kasuwaci tsakanin Indiya da Afirka
October 24, 2015Talla
Taron wanda shi ne irinsa na uku kuma mafi girma da Indiya din za ta jagoranta zai maida hankali ne kan yaukaka huldar cinikayya da kuma diflomasiyya tsakanin kasar da kasashen Afirka.
Masu aiko da rahotanni suka ce baya ga batun cinikayya, taron har wa yau zai tabo abubuwan da suka danganci makamashi da tsaro da kuma magance dumamar yanayi.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da China wadda ke kan gaba ta fuskar cinikayyya da Afirka ta bayyana cewar ta na samun koma baya na cigaban tattalin arzikinta, lamarin da ya sanya ake ganin za ta ja baya kan hulda da kasashen Afirka a fage na kasuwanci.