Taron G20 a Brazil
November 18, 2024A wannan Litinin shugabannin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na duniya, na kungiyar G20, suke fara taron kwanaki biyu a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, inda shugabannin daga kasashe da ke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya za su tattauna, kuma daya daga cikin batutuwan shi ne hanyar dakile matsanancin talauci a duniya.
Karin Bayani: G20: Scholz ya jaddada goyon baya ga Isra'ila da Ukraine
Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva na kasar Brazil mai masaukin baki yana son amfani da wannan dama wajen karfafa batun yaki da yunwa da kuma talauci a duniya. Taron na kungiyar G20 ya kunshi shugabannin da suka hada da Shugaba Joe Biden na Amurka, da Xi Jinping na Chaina, gami da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, yayin da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ba zai halarci taron ba, amma ya tura ministan harkokin wajen kasar. An kuma gayyaci kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar Tarayyar Afirka.