Taron jammiyyar SPD
January 6, 2007Talla
Magabatan jammiyyar SPD dake nan Jamus na gudanar da taro a birnin Bremen,domin tattauna makomar tsare tsaren kasar.Jammiyyar wadda ke gwamnatin hadin gwiwa da jammiyar masu raayin mazan jiya , akarkashin jagorancin Angela Merkel ,na samun matsin lamba daga wasu dake cewa ,tana rasa makomar ta na siyasa awannan kasa.Batutuwa muhimmai biyu da ake tattaunawa a taron na jammiyar SPD ,na yini biyu dai sun hadar da gyare gyaren harkokin lafiya da kasuwar kwadago.