Taron Afrika kan matsalolin kan iyaka a Yamai
May 17, 2012
Kanta Tun ranar litinin ɗin da ta gabata ne ƙwararrun masana daga ƙasashen Afrika kusurwa huɗu suka gudanar zaman taron sharen fagen taron ministotin a birnin Yamai, wanda suka zaiyana irin matsalolin dake da akwai akan iyaka, da kuma matakan da yakamata a ɗauka don magance su.
Ƙungiyar tarayya ƙasashen Afirka wato AU a 2007 a birnin Adis Ababa ƙasar Habasha ta gudanar da wani taron yin nazarin ɗaukar matakan shawo kan rigingimun iyaka tsakanin ƙasa da ƙasa. Malam Abdu Labo,ministan kula da harkokin cikin gida na niger,ya bayyana kadan daga cikin matsalolin iyakokin.
"Na farko shiga kasar makofta wato batun visa, sannan batun iyakokin kansu, ita taraiyar Afrika ta wannan gadon iyakar da turawan mulkin mallaka da suka barma ƙasashen Afrika ko da babu daɗi ayi haƙuri a zauna hakanan. Amma wasu ƙasashe sun yi gajen haƙuri wanda ma take kai su darewa bayu".
Galibi gadon shata iyakar da aka daga turawan mulkin mallaka ne yake haddasa rigingimu in har ba a kai zuciya ne sa ba. Kanal mai ritaya Mahamman Karau shine shugaban hukumar kula da shata iyakar niger tsakanin ta da makoftanta.
Ya ce "Takardu sun ce haka wannan ƙasar ta kiya wanccan ta kiya ita, sai abin ya kai ga alkalancin kotun duniya, kamar yanda ta kasance tsakanin Nijar da ƙasar Benin. A yanzu haka ana jiran wani alkalancin kotun duniya tsakanin Nijarr da ƙasar Burkina Faso. Irin waɗannan abubuwan sune ƙungiyar taraiyar Afrika take son ta kiyaye aukuwar su".
Hanyoyin warware rigingimu
Mafi kyau idan har an sami irin waɗannan rigingimun a maimakon faɗace-faɗace akwai hanyoyin gyara cikin lumana, kamar yanda minista Abdu Labo ke cewa.
" In ƙasashen da suke rigima ana son su gyara matsalar su cikin ruwan sanyi, amma in abin ya ci tura to a garzaya zuwa kotu don ta yi alkalanci, kuma kowa ya yarda da wannan hukuncin".
Rigimgimun dai suna maida hannun agogo baya, shine ƙungiyar taraiyar ƙasashen Afrika ke fatan waɗannan rigingimun su kau don a maida hankali wajen tattalin arzikin ƙasashen Afrikan.
Mawallafi: Mahamman Kanta
Edita : Zainab Mohammed Abubakar