Tarihin dakarun Amirka a Jamus
Tsawon shekaru 75 sojojin Amirka ke Jamus. Sun zo ne a matsayin wadanda suka yi nasara a yakin duniya na biyu sun kuma kasance kawaye. Sai dai dangantakar ba ta kasance mai kyau a kullum ba.
Ziyara daga manyan mutane a filin jirgin saman sojoji na Ramstein
Kusan sojojin Amirka dubu 35 aka girke a Jamus, akasarinsu a yammaci da kudancin kasar. Babu wata kasa a Turai da ke da yawan sojojin Amirka kamar Jamus. Hakan zai canza, domin shugaban Amirka Donald Trump zai janye sojoji dubu 12 daga Jamus. Hakan na zama wata tawaya ga kawancen sojoji tsakanin Jamus da Amirka.
Daga masu galaba zuwa masu ba da kariya
Yakin duniya na biyu ya kasance mafarin kasancewar sojojin Amirka a Jamus. A shekarar 1945 Amirka da kawayenta guda uku sun 'yantar da Jamus daga mulkin 'yan Nazi, amma cikin sauri tsohuwar kawa ta yaki wato Tarayyar Soviet ta zama sabuwar abokiyar gaba. Ba da dadewa ba tankokin yakin Amirka da na Sobiet sun tsaya daura da juna a Berlin da aka raba gida biyu.
Sojan Amirka Elvis Presley
Tare da sojojin Amirka an kuma samu yaduwar al'adun Amirka a Tarayyar Jamus. Sarkin salon kidan "Rock 'n' Roll", kamar yadda daga baya ake kiran Elvis Presley, da shi kanshi sojan Amirka ne. A shekarar 1958 ya fara aikin yi wa kasa hidima a fannin sojan Amirka a Jamus. A nan yana daga wa mabiyansa hannu a tashar jirgin kasa ta Bremerhaven.
Unguwarsu
Wani sojan Amirka ke nan tsaye a wata hanyar da ke unguwar sojojin Amirkan da ke filin jirgin sama na Wiesbaden-Erbenheim. A kewayen sansanin sojin na Amirka akwai unguwanni na sojojin Amirkan da kuma iyalansu. Wannan ya sa sajewarsu cikin al'umar Jamusawa ta yi wahala. Fararen hula Amirkawa kimanin dubu 17 ne rundunar sojin Amirka ta ba wa aiki a Jamus a shekarar 2019.
Haduwa tsakanin mutane
Duk da zama a unguwanni dabam-dabam, da farko an yi ta haduwa don nishadi tsakanin iyalai Jamusawa da Amirkawa. A shekarun farko ana haduwa a cashe lokacin bazara a kan titunan birnin Berlin sannan a lokacin sanyin hunturu sojojin Amirka na shirya bikin Kirsmetti ga yaran Jamusawa. An samu kuma makon abokatanka tsakanin Jamusawa da Amirkawa.
Shawagi tare da rundunar Bundeswehr
A lokacin yakin cacar baka sansanin da ke yammacin Jamus ya samu muhimmanci na musamman. NATO ta yi atisaye da ake kira "Reforger I" wato dawowar dakaru a Jamus, wanda ya kankama a Vilseck/Grafenwöhr a shekarar 1969. A lokacin Amirkawa sun yi atisaye da dama tare da rundunar sojan Jamus ta Bundeswehr. Jamus tana a rabe. Tarayyar Sobiet da kawayenta na cikin kawancen Warsaw sune abokan gaba.
Takaddama kan rokokin nukiliya
Karkashin gadi mai tsanani a 1983 an kai rokokin Pershing-II zuwa sansanin sojin Amirka da ke Mutlangen. Rokokin masu dauke da bama-baman nukiliya sun dauki hankalin jama'a. Da sune za su cike gibi a matakan tsoratarwa da NATO ta yi wa yarjejeniyar Warsaw. Sai dai matakin na zaman lafiya ya zama wata barazana ya kuma ci karo da zanga-zangar da mashahuran mutane suka shiga ciki.
Yakin Iraki ya raba kan Amirka da Jamus
Kimanin shekaru 20 baya, shugaban Amirka George W. Bush ya kaddamar da yaki kan Iraki saboda zargin ta mallaki makaman kare dangi. Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya ki tura sojojin Jamus cikin yakin ya kuma samu goyon bayan daukacin Jamusawa. Takaddamar ta janyo tsamin danganta tsakanin gwamnatocin guda biyu.
Jamus ta ci gaba da zama sansani mai muhimmanci
Ko bayan an janye sojojin Amirka dubu 12.000, kamar yadda Trump ya yi niyya, Jamus za ta ci gaba da zama muhimmiya ga muradun tsaron Amirka. Sansanin sojin Amirka na Ramstein na taka muhimmiyar rawa ta musamman na zama shalkwatar rundunar sojin saman Amirka a Turai. Daga nan ake juya akalar jiragen sama marasa matuka da ke yaki da 'yan ta'adda a Afirka da Asiya.