Tana ƙasa tana dabo game da shari'ar Kenyatta
February 6, 2014Shari'ar shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyata wanda a yanzu haka ke gaban kotun hukunta manyan laifukan yaƙi dake The Hague, na barazanar rushewa sakamakon rashin shaidun da za su fito su ƙarfafa zarge-zargen da kotun ke tuhumarsa da su. A yanzu haka dai kotun na ƙoƙarin mayar da martabarta a Nahiyar Afirka, inda yawancin ƙasashen ke ƙoƙarin zamewa daga yarjejeniyar da suka ƙulla da ita tun farko.
Ranar laraba ta sake kasancewa ranar da ta ƙara jefa masu shigar da ƙara a shari'ar shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta cikin takaici, wannan ne lamari mafi kunyatarwa ga masu shigar da ƙarar a tarihin kotun na shekaru 12, domin sun sake zuwa gaban alƙali basu da shaidu ko ɗaya a hannu. Ana tuhumar Kenyatta ne da aikata manyan laifukan yaƙi, bayan da rikici ya ɓalle a ƙarshen zaɓukan ƙasar da aka yi a watan Disemban shekara ta 2007.
Masu gudun hijira sun gaza komawa gida tun 2007
A lokacin rikicin dubai suka rasa rayukansu kuma har yanzu da yawa na gudun hijira a ƙasashe maƙota kuma suna tsoron komawa gida duk da cewa ana zaman kwanciyar hankali.
Waɗanda ke goyon bayan Kotun na hukunta manyan laifukan yaƙi a Afirka na ganin cewa kotun na da laifi wajen samun abin da take gani yanzu, domin tilas ne Kenyatta ya kasance a wannan shari'a kamar yadda Chris Peter wani farfesa a sashen kula da haƙƙin ɗan adam a jami'ar Daresalaam dake Tanzaniya ya bayyana
Ana tuhumar shugaban ƙasar Kenya, saboda haka akwai buƙatar ɗaukar shi a matsayin wanda ake tuhuma, kuma idan har aka sake mi shi da yawa, zai sami zarafin jujjuya abubuwa yadda zasu taimake shi, kamar yayi wasa da hanakalin shaidu, ya ma yi ƙoƙarin samun goyon bayan mutane, domin ya riga ya fara samun goyon bayan ƙungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya da sauransu.
Har a Majalisun ƙasarsa dai Kenyatta ya nemi wannan goyon baya, kuma a dalilin wannan goyon bayan da ya yi ƙoƙarin samu dai har an riƙawa kotun laƙabi da karen farautar ƙasashen yamma, Kusan abu guda ne ake gani a shari'ar shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir, wanda shi ma ake tuhumarsa da aikata laifukan yaƙi amma duk da takardar sammacin ƙasa da ƙasa da aka fitar, har yanzu babu abin da ya faru.
Ko da shi ke manazarta na ganin cewa babban kuskuren da kotun ta yi tun kafa ta shi ne ba ta da masu bincikenta a ƙasashe ko kuma ma jami'an tsaro dole ne ta sami hukumomin da zata iya aiki da su a cikin ƙasashe kamar dai yadda Andreas Zimmerman ƙwararre a kan manyan laifuka dake jami'ar Postdam ya bayyana.
Babu wata barazana ga Omar Al Bashir na Sudan
"Shugaban ƙasar Sudan Omar Al Bashir ne kaɗai ke zuwa zuci wanda ake tuhumarsa da laifukan yaƙi, kuma idan har Sudan duk da cewa ta yi amanna da Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya bata ba da haɗin kai ga kotun hukunta manyan laifukan yaƙin ba, kuma Kwamitin Sulhu da sauran ƙasashe ba su matsawa Sudan lamba, domin a iya samun wannan haɗin kan".
Ɗaya daga cikin masu shigar da ƙarar Benjamin Gumpert, mahukuntan Kenyan ke janyo tsaiko a binciken suna riƙe mahimman takardun da ake buƙata misali wasu daga cikin takardun shiga da fitan kuɗaɗe, inda Mr Gumbert ke cewa idan an duba za a sami hujjar cewa shugaban ƙasa ya biya wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa. Haka nan kuma mahimman shaidu a 'yan makonnin da watannin da suka gabata sun janye. Chris Peter na jami'ar Daresalaam a Tanzaniya ya yi mana ƙarin bayani
"A tunani na dole ne kotun ta sake yin bitar wannan hukuncin da za ta yanke a wannan shari'a domin wannan mutumi ne wanda wataƙila, kuma ina taka tsan-tsan wajen amfani da wannan kalma, wanda za a wanke ba dan cewa ba shi da laifi ba, amma dan babu wanda zai iya bada shaida. A taƙaice ma ba mutumin da bashi da laifi ba ne ake tuhuma, mutun ne wanda wanda a shari'arsa shaidu suke ɓatar dabo"
Chris Peter na Jam'ar Daresalaam da takwararsa Andreas Zimmerman na Jami'ar Postdam na ganin cewa duk ma me a ke ciki hukuncin da kotun za ta yanke kan wannan shari'a zai yi tasiri kan duk abin da zai biyo baya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh