1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirya fina-finan Nollywood a Najeriya

Zulaiha Abubakar
May 16, 2019

Legas guda cikin jihohin Najeriya a fannin kasuwanci yanzu haka ta samar da jami'o'i 13 wadanda zasu horas da sabbin masu shirya-fina fanan da za a dinga kwatance dasu.

https://p.dw.com/p/3IbF7
Kamerun Buea  Cameroon International Film Festival Zack Orji
Hoto: DW/A. Kriesch

Masana'antar shirya fina-finai ta Najeriya watau Nollywood na fidda fim din da yawansa ya kai 1,500 duk shekara kasancewar ta biyu a duniya a harkar fim.

Temitope kenan mai shekaru 21 a lokacin da yake gwajin yankin wani fim za zaiyi,dalibin jami'ar wasan kwaikwayo daje jihar Lagos, burinsa shine ya zamo shahararren 'dan fim.

"Babu wani abu a rayuwa dake samuwa cikin sauki, sai kayi watsi garin ku ka manta da komai don cimma burinka ,ina matukar son nishadantarwa don haka na tunkare ta na manta da komai".

Awanni biyu ya rage a janye labule don fara fim,amma shugaban shirin Toyusi Tejumade Morgan bai gamsu ba.

"Ku maimaita,har yanzu kana kallon Amanda".

To sai dai duk irin wahalar dake tattare da shirin fim Temitope ya ce bakin rai bakin fama, ya dauki aniyar cika burunsa na ganin ya zama fitaccen tauraro a Nollywood watau shaharariyar masana'antar fim din tarayyar Najeriya .kamar yadda wani dalibi yayi karin haske.

Ana daukar fim
Ana daukar fimHoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

"Misalin idan ina tsaka da wasa a kan munbari ,wani daga cikin masu shirya fina-finai ya ganni ,zai iya cewa na birgeshi don haka zai jarraba ni a shirin sa, nan guri ne da jama'a da dama ke halarta wannan wurin wadanda suka hada da fitattu taurari".

Daga cikin wadanda suka halarci wannan guri akwai iyayen 'dan wasan wadanda ke son ganin dansu ya fara fim a karon farko ga mahaifin Temitope Morgan.

"Ban taba ganin sa yana fim ba,don haka nazo in ganewa idona ina fatan  yafi kowa fice  wasan".

An kebe wani lokaci bayan shirye-shiryen fim din don musayar ra'ayi tsakanin 'yan kallo da masu shirin,don karawa jama'a kaunar harkar fina-finaninda akan tabo batutuwan dasuka shafi tunani da nishadantarwa.