Take-take irin na kama karya a Kenya
December 19, 2014A yau zamu fara ne da labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta game da kasar Kenya tana mai cewa an doshi hanyar kama karya.
Ta ce a wani abin da ke kama da fakewa da guzuma a harbi karsana, gwamnatin Kenya ta yi amfani da yaki da ta'addanci a matsayin hujjar janye izinin gudanar da aiki na kungiyoyin agaji fiye da 500, sannan a lokaci daya ta gabatar da daftarin doka da bisa ga dukkan alamu zai takaita 'yancin jama'a. Jaridar ta ce har yanzu kasar Kenya da ke gabashin Afirka na da kyakkyawan suna wajen tabbatar da 'yancin 'yan jarida da hakkin jama'a. To amma kasar karkashin shugaba Uhuru Kenyatta ta kama hanyar yin fatali da wannan 'yanci, bisa hujjar cewa matsalolin ta'addanci da kasar ke fama da su ya zame mata dole ta dauki matakan kariya. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka ce Kenya ta kama hanyar zama wata kasa ta kama karya.
Matakin koma wa da 'yan M23 gida ya ci-tura
Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta mayar da hankali ne a kan matakin komawa da tsaffin 'yan tawayen Kongo gida daga Yuganda, tana mai cewa aikin komawa da 'yan kungiyar M23 ya kare cikin yamutsi.
Ta ce kokarin mayar da 'yan tawayen Kongo na kungiyar M23 su kimanin 1400, gida, ya gamu da cikas, inda wadanda ke iyawa suka tsere zuwa wata maboya. Yanzun haka dai mayaka 100 kadai ne aka yi nasarar kai su filin jirgin saman garin Entebbe. Tun sama da shekara guda ke nan 'yan tawayen na M23 suka samu mafaka a Yuganda, bayan sun tsere daga filin fafatawa da sojojin Kongo a watan Nuwamban shekarar 2013. Wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin gwamnatin Kongo da 'yan tawayen a watan Disamban 2013, 'yan tawayen sun yi alkawarin ajiye makamai sannan su kafa jam'iyyar siyasa. Gwamnati ta yi alkawarin yi musu afuwa. Amma hakan bata samu ba. 'Yan tawaye 400 daga cikin 1600 suka ci gajiyar wannan shiri. Saboda rashin sanin makomarsu 'yan tawaye sun tsere daga sansaninsu a Yuganda zuwa tudun mun tsira.
Bikin Kirsmetti da cutar Ebola
Daga yankin yammacin Afirka kuwa jaridar Neues Deutschland ce ta yi tsdokaci game da cutar Ebola da har yanzu ke ta'adi a wannan yanki.
Ta ce kasar Saliyo ta fito fili ta haramta bukukuwan Kirsmetti da na sabuwar shekara a bainar jama'a saboda cutar Ebola. Wannan matakin dai zai fi shafar kananan yara, wadanda musamman ake ci da guminsu wajen sa su aikin karfi domin makarantu na rufe. Ko da yake addinin Musulunci ya fi kowane addini yaduwa a fadin kasar, amma ana gudanar da bikin Kirsmetti. Sai dai a bana za a ga bambamci domin shugaban kasa Ernest Bai Koroma ya yi kira ga shugabannin al'umma da su yi hakuri a bana su yi watsi da gudanar da bikin na shekara-shekara a wani mataki na yaki da bazuwar kwayoyin cutar Ebola. Saliyo ke kan gaba wajen yawan masu fama da Ebola a yankin yammacin Afirka. Ya zuwa yanzu mutane fiye da 8000 a Saliyo suka harbu da cutar inda kimanin 1900 suka mutu.