Takaddamar yankin Kurdawa na Iraki
October 11, 2017Talla
Wani babban jami'n kotun kolli na Irakin ya ce wadanda suka shirya zaben sun taka doka, bayan da babbar kotun ta dakatar da zaben gabanin ma a yi shi a cikin watan Satumbar da ya gabata. Makonnin biyu dai da yin zaben raba gardamar na yankin Kudawan wanda ya samu nasara har yanzu ana kai ruwa rana tsakanin hukumomin Bagadaza da na Erbil cibiyar yankin na Kurdawa.