Najeriya: Samar da 'yan sandan jihohi
April 23, 2024Wannan dai ya nuna sha'awar gwamnati a kan lamarin, bayan da sifeto janar na 'yan sandan Tarayyar Najeriyar Kayode Egbetokun ya bayyana adawarsa da kafa 'yan sandan jihohi bisa cewa Najeriya bata kai matsayin hankali ko balagar da za ta kafa su ba. ya bayyana adawa da kokarin samar da 'yan sandan jihohin. Wannan batu na bukatar samar da 'yan sanda na jihohi a Najeriyar yana kara amo ne sosai a yanzu, saboda lalacewar al'amura na tsaro a kasar da ya kai ga sanya al'umma daukar matakai na kare kansu daga hare-hare musamman na 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
Tuni dai majalisar wakilan ta Najeriyar, ta yi wa bukatar sauya dokar 'yan sandan karatu na biyu. Samun adawa daga bangaren 'yan sanda babban al'amari ne a wannan kacaniya da ake yi, inda aka kai wannan matsayi na jin ra'ayin jama'a dangane da batun kafa rundunar. Ga kwararru a harakar kamar Dakta Kabiru Adamu shugaban cibiyar Beacon da ke aiki a fanin tsaro a Abuja, ya ce akwai abin da ake tsoron faruwarsa. A yayin da ake ci gaba da muhawara a kan wannan batu akwai alamun da sauran aiki a gaba, domin a yanzu da aka samu wannan mataki za a koma ga sauraron jin ra'ayin jama'a a majalisa su yanke hukunci kafin aika dokar a zuwa jihohi domin neman amincewarsu.