Chaina ta yi barazana wa 'yan Taiwan saboda zabe
January 13, 2024Talla
'Yan takara guda uku ne dai ke fafatawa a zaben a ciki har da shugaban mai barin gado Tsai Ing-wen. Mataimakin shugaban kasar Lai Ching-te na jam'iyyar DPP, wanda ake hasashen zai samu nasara, Chaina na yi masa kallon babban hadarin saboda manufofinsa na samun yanci Taiwan din. Yanki mai yawan al'umma miliyan 23da ke da tazarar kilomita 180 daga gabar tekun kasar China, ana yaba masa a matsayin abin koyi na dimokuradiyya a nahiyar Asiya: Zaben da zai kammala tun zagayen farko, tuni da aka bude runfuna zabe da karfe takwas agogon GMT kuma za a rufesu da misalin karfe hudu ,tare da sa ran samun sakamakon zaben da yaTaiwan da Chaina rikici na ta'azzaramma.