Kasashen Libiya da Marokko cikin alhini
September 14, 2023Kasashen biyu da dukansu ke yankin Arewacin Afirka sun tsinci kansu cikin halin alhini, sakamakon bala'o'in girgizar kasa da ambaliyar ruwa da suka afka musu. Mummunar girgizar kasa da ta janyo asarar dimbin rayuka da dukiyoyi ce ta fara afkuwa a Marokko, kafin daga bisani makwabciyarta Libiyata tsinci kanta cikin ibtila'in ambaliyar ruwa.Rahotanni sun nunar da cewa duk da yanke kauna da samun wadanda suke da sauran numfashi a karkashain barakuzan gine-gine a Marokko har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da lalube tare da kokarin kai dauki ga wadanda abin ya shafa, a daidai lokacin da aka samu motsin kasa a garin Imi N'tala da ke wajen birnin Marrakesh da girgizar kasar ta shafa.
A kasar Libiya kuwa da za a iya cewa tana da gwamnatoci biyu, masu aikin agaji na fuskantar kalubalen isa ga wadanda ke tsananin bukatar tallafi. Rahotanni sun nunar da cewa wasu masu aikin agaji da suka riga suka shiga cikin birnin Derna da ambaliyar da ta afku sakamakon mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Daniel ta fi shafa, sun shaidar da ganin gawarwaki a warwatse a kan tituna da cikin gidaje ko kuma suna iyo a cikin ruwan da ke kwarara. Tuni dai kasashen duniya suka fara sanar da kai kayan agajin da aka fi bukata zuwa kasashen biyu.