Masarautun gargajiya na zama tushen shugabanci da jagorancin al'ummar arewacin Najeriya, wanda ko a zamanin Turawan mulkin mallaka an ga yadda suka tafi tare da su. Sarakuna kan zamo alkiblar al'umma ta fuskar gudanar da rayuwa da dukkan al'amura na yau da kullum, kama daga harkokin neman ilimi da kasuwanci da zamantakewa da sana'o'i da dukkan lamuran da suka shafi al'adu da ma addinai.