Adawa da matakin karin wa'adin mulki
April 26, 2021Dandazon mutane ne suka yi ta maci suna nuna rashin jin amincewarsu da ci gaba da zama a kan mulkin kasar da Shugaba Mohammad Abdullahi Farmajo ke yi bayan karewar wa'adinsa na mulki a makonnin da suka gabata.
Bayanai daga Somaliya dai na cewa ne an yi ta jin karar harbe-harbe ne a jiya Lahadi, inda sojoji suka rufe galibin manyan hanyoyin Mogadishu babban birnin kasar.
Shugaban Somaliya Mohammad Abdullahi Farmajo dai ya kara wa'adin nasa na mulki bayan karewar wa'adinsa a hukumance cikin watan Fabrairun da ya gabata.
Wasu daga cikin 'yan kasar sun ce harbe-harben da aka yi ta jin su dai na manyan makamai ne da ake ganin rokoki ne gami da ratsin wasu na kananan bindigogi, wadanda suka suka ci gaba har cikin dare.
Wani mazaunin birnin Mogadishu ke nan, Abdullahi Mahdi, ke cewa, "galibinmu a wannan kasa ba mu yarda da karin wa'adi da gwamnati ta yi wa kanta ba. Hakan zai iya jefa kasar nan cikin wani sabon yaki. ZAnga-zangar lumana za ta ci gaba da kasancewa a nan. Sai dai su kuwa sojoji suna ci gaba da jan daga. Wannan ne zai sake sanya kasar nan bisa turbar yakin basasa."
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon shugaban Somaliyar, Hassan Sheikh Mohammad, ya zargi shugaba mai ci, Abdullahi Farmajo da aika dakaru yankin da yake, daidai lokacin da adawa ke kara zafi a kan ci gaba da zama kan karagar mulki da shi Faramajo ke yi a kasar da ke kan hadarin iya birkicewa saboda hali na rashin tsaro da take ciki.
Wasu rahotannin ma sun tababtar da cewa an samu bambancin ra'ayi a tsakanin dakarun kasar, inda ake dora alhakin harbe-harben a kan bangarori da ba su jituwa a cikin su, musamman na birnin Mogadishu.
Nan kuma Abshir Shu'ayb ne, ke fadin, "yau mun taru a nan Mogadishu don ci gaba da jaddada wa gwamnati matsayinmu a kan cewa ba mu son mulkin kama karya a Somaliya. Shugaba Farmajo na son dorewa a kan mulki ta karfin tsiya. Muna iya yi wa wasu daga cikin jami'an soji da suka kyale mu muna zanga-zanga ta lumana a nan".
A tsakiyar wannan watan ne dai Shugaba Abdullahi Farmajo, ya tsawaita wa'adinsa a mulkin, bayan sanar da shirin zaben da daga bisani aka dage, inda a yanzu ya kara wa kansa wa'adin mulki na wasu shekaru biyu.
Tuni wasu ke bayyana hakan a matsayin wani abin da zai kara ta'azzara rashin tsaro, bayan wanda dama ake fama da shi na tarzomar yakin da mayakan al-Shabaab suka kunnaa kasar da ke a kuryar Afirka.
Kungiyar al-Shabaab dai kungiya ce da ta yi kaurin wajen wajen alaka da manyan kungiyoyin ta'adda na duniya kamar su al-Qaeda da IS.
Somaliyar kasa ce da ta yi fama da yakin basasa a shekara ta 1991, abin da ya haddasa asarar rayuka na mutane da dama wasu miliyoyi kuma suka rasa sukuni, inda har yanzu wasu dubban 'yan kasar ke a kasashe a matsayin masu zaman mafaka.