Rikici a zauren majalisar dokokin sudan ta Kudu
June 20, 2019Talla
A lokacin da suke yi wa maneman labarai karin haske game da ficewar tasu, 'yan majalisar sun bayyana rashin biyan albashin ma'aikata da sojojin kasar a matsayin dalilin da ya sanya su yin bore. Sun kuma bayyana yadda sojojin kasar a yanzu suka rungumi sare bishiyoyi don sayar da itace a matsayin hanyar da suke samun kudin shiga.
Tuni dai kakakin majalisar ya sanar da dage zaman majalisar zuwa wani lokaci don yin duba game da korafin 'yan majalisar. Tun a watan Mayun da ya gabata ne bangaren gudanarwar kasar da kuma jam'iyyun adawa suka amince da karin watanni shida kafin kaddamar da gwamnatin hadaka a wani bangaren cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta sudan ta Kudu.