1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Stoiber zaiyi Murabus daga shugabancin CSU

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuU9

Majiya daga jammiyar kawancen shugabar gwamnati Angela Merkel ,ta CSU dake nan jamus na nuni dacewa shugaban jammiyyar kuma premiern jihar Bavaria Edmund Stoiber ya amince da murabus daga mukaminsa cikin wannan shekara.To sai dai wani babban jamiin jammiyar ya karyata wannan batu.Mr Stoiber dai ya kasance shugaban jammiyyar ta Christian Social Union,na tsawon shekaru da dama da suka gabata,jammiyar dake kawance da CDU ta Merkel a gwamnatin ta,mutuminda kuma kadan ya hanashi lashe zaben shekarata 2002.Sai dai taurarin Stouber sun fara dasashewa ne sakamakon wani rikicin daya barke tsakaninsa da wani abokin adawa.Kafin wannan lokaci da ake ciki dai,an kyautata zaton cewa Mr Stoiber mai shekaru 63 da haihuwa zai sake takaran kujerar premiyan jiharsa ta Bavaria a shekara mai kamawa.