SPD ta tsayar da Scholz takara a 2021
May 9, 2021A yayin wani muhimmin taro da wakila 600 na wannan jam'iyyar da ke cikin gwamnatin kawance ta Jamus ta gudanar da intanet a birnin Berlin, tsohon magajin garin Hamburg Olaf Scholz ya sami kuru'u mafi rinjaye na kashi fiye da 96 cikin 100.
Daga cikin manufofin da ya sa a gaba a gangamin yakin neman zaben na majalisar dokoki, Olaf Scholz ya yi alkawarin sauya alkiblar tattalin arziki tare da kawo ci gaban muhalli da cimma manufar sauyin yanayi nan da shekarar 2045. Kana ya gabatar da wasu manufofi na kawo ci-gaba a fanonin kiwon lafiya da illimi da kuma sufuri.
Sai dai jam'iyyar SPD Jam’iyyar na samun koma baya a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya-bayannan, inda za ta iya samun kashi 16 daga cikin 100 na kuri'u a zabe mai zuwa, yayin Jam’iyyar Greens da CDU ta Merkel suka kasance a gabanta a fadin kasar.