SPD: Sabon shugaba
November 15, 2005Jam’iyyar SPD ta nan Jamus, ta sami sabon shugaba. A taron da `yan jam’iyyar suka kammala jiya a birnin Karlsruhe ne, suka zabi Matthias Platzeck, Firamiyan jihar Brandenburg tamkar sabon shugabansu, wanda zai maye gurbin Franz Müntefering. A jerin masu binciken ra’ayin jama’a dai, Mattias Platzeck, ba sananne ba ne. Amma watakila hakan zai sake. Shi dai Platzeck, yana da shekaru 51 da haihuwa, kuma shi ne dan gabashin Jamus na farko da ya taba shugabancin jam’iyyar. Bayan an zabe shi a taron da jam’iyyar ta yi jiya a birnin Karlsruhe, ya bayyana a cikin farkon jawabinsa cewa:-
„Ina farin cikin wannan aminci da kuka nuna mini. Zan kuma yi duk iyakacin kokarina wajen dukufad da lokacina ga jam’iyyar ta Social Democrtas. Amma ta yadda zan iya ci gaba da aikina tamkar Firamiyan jihar Brandenburg.“
Tun cikin shekara ta 2002 ne dai aka zabi Platzeck tamkar Firamiyan wannan jihar, don ya maye gurbin Manfred Stolpe. Kafin hakan dai, Platzeck, shi ne ke kula da ma’aikatar kare muhalli ta jihar. A cikin shekarar 1998 ne ya tsaya takarar zaben magajin birnin Potsdam, inda kuma ya ci nasara. Kololuwar nasarorin da ya samu a fannin siyasa dai, ita ce sake zabansa da aka yi, a mukamin Firamiyan a shekarar bara. Jam’iyyarsa ta SPD kuma, ita ce ke da rinjayi a majalisar jihar ta Brandenburg.
Ana dai kyautata zaton cewa, a fagen siyasar tarayya ma, zai nuna irin kwazon da ya nuna ne a jiharsa ta Brandenburg, abin da ya janyo masa farin jini, har ma a gun `yan jam’iyyun adawa. Matthias Paltzeck, ya bayyana cewa, yana goyon bayan gwamnatin hadin gwiwa ta taryyar da aka cim ma yarjejeniyar kafawa, kuma zai ba da tasa cikakkiyar gudumowa, wajen ganin cewa ta sami nasara.
A jiharsa ta Brandenburg dai, kwarjinisa na ta kara yin sama, saboda irin matakan farfado da tattalin arzikin jihar da ya gabatar, wadanda kuma yake aiwatarwa da samun nasara.
To yanzu dai gagarumin kalubalen da ke gabansa, shi ne yadda zai jagoranci jam’iyar ta SPD, a daidai lokacin da take husakantar rikice-rikice a bainar `ya`yanta.