1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a wani Otel ya yi sanadiyyar rayuka

Binta Aliyu Zurmi
October 23, 2022

Wani harin ta'addanci da mayakan Al-Shabaab suka kai a wani Otel da ke kudancin kasar Somaliya ya yi sanadiyar rayukan mutane 4 a cewar shaidun gani da ido.

https://p.dw.com/p/4Ia0j
Hoto: Str./AFP

Jami'an tsaro da suka tabbatar da harin, sun ce mota shake da ababen fashewa ta kutsa cikin Otel din Tawakal a garin Kismayo a wannan Lahadi.

Wannan harin dai bai zo da mamaki ba don ko baya ga jami'an gwamnati da mayakan na Al-Shabaab suka saba kai wa farmaki sukan yi hakan a kan fararen hula a cewar wani jami'in 'yan sanda Abdullahi Isma'ail.

Sama da shekaru 15 ke nan kungiyar Al-Shabaab ke kokarin kifar da gamnatin farar hula a kasar, inda ta ke kai harin kan mai uwa da wabi a kan jami'an tsaro da kuma al'umma.

A shekarar 2019 an kai wani hari makamancin wannan a wani Otel da ya salwantar da rayukan mutum sama da 20 tare da jikkata wasu mutum 117.