1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya halaka mutane a Somaliya

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 25, 2021

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama cikin har da kananan yara suka jikkata a Somaliya, sakamakon harin da aka kai da abubuwa masu fashewa a Mogadishu babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/43TRV
Somalia | Sprengstoffanschlag in Mogadischu
Somaliya na shan hare-hare daga kungiyar ta'addan Al-ShabaabHoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture alliance

Rundunar 'yan sandan kasar ce ta tabbatar da afkuwar harin, inda ta ce daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu har da dan kunar bakin waken da ya kai harin. Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan Al-Shabaab da ta addabi kasar ta Somaliya cikin wata sanarwa a gidan radiyon Andalus mallakarta, ta dauki alhakin harin da aka nufi kai wa a sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU da ke birnin na Mogadishu.