1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke zaben Kenya ya mamaye jaridun Jamus

Ramatu Garba Baba
September 8, 2017

Har yanzu dai soke zaben shugaban kasar Kenya da kotun kolin kasar ta yi a makon da ya gabata na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon, baya ga batun ambaliyar ruwa a wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2jai8
Kenias Oberstes Gericht
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Azim

 

A labarin da ta buga mai taken Sauyin rawa a Kenya jaridar Süddeutche Zeitung ta fara ne da cewa ba a dauki lokaci mai tsawo ba kafin Shugaban Kenya Uhuru Kenyata ya fara yakin neman zabe bayan da a jawabinsa ta gidan talabijin ya ce zai mutunta hukuncin kotun kolin kasar, amma kuma kwana guda ya fito karara ya soki lamirin babban mai shari'a na Kenya David Maraga kana kuma ya ce akwai matsala a tsarin shari'ar kasar da ya zama dole a yi gyara. Shi kuwa a nasa bangaren madugun 'yan adawa Raila Odinga kira ya yi da a yi wa hukumar zaben kasar garambawul. Sai dai jaridar ta saka ayar tambaya tana mai cewa ko za a sake yin amfani da tsarin zaben kasar mai cike da rudani.

Kenia Nairobi Wahlen Stimmenauszählung
Al'ummar Kenya za su sake zaben shugaban kasa bayan kotun koli ta soke zaben farko.Hoto: Reuters/T. Mukoya

Gagarumin ci-gaba ga nahiyar Afirka inji jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhin da ta yi game da soke zaben na Kenya. Ta ce a karon farko a Afirka wata kotun koli ta soke zaben shugaban kasa sannan ta ba da umarnin a gudanar da sabon zabe. Sai dai wannan lamarin ya auku ne a Kenya kasar da ta zama abin koyi, kafin matsalolin cin hanci da rashawa da rikicin kabilanci su zama ruwan dare a cikin al'amuran kasar.

Mali Soldaten
Shirin daukar matakai kan wadanda ke kawo tarnaki a zaman lafiya a MaliHoto: Getty Images/AFP/J. Saget

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Mali, inda Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da sabon kudurin sanya takunkumai kan masu kawo cikas ga shirin wanzar da zaman lafiyar kasar. Jaridar ta ce a shekarar 2015 ma Kwamitin Sulhun ya yi barazanar sanya takunkumai kan wadanda ya kira masu hana ruwa gudun a Mali, amma har yanzu ya kasa aiwatar da matakin saboda adawa daga bangaren gwamnatin Mali. Sai dai wani roko a hukumance da ya fito daga gwamnati a birnin Bamako a makon da ya gabata, ya sauya al'amura. Babu tabbas ko wannan sabon mataki na barazanar sanya takunkuman zai samar da zaman lafiya a Mali, domin a ranar Laraba 'yan tawayen Abzinawa sun kai hari kan wata motar sojojin gwamnati da suka je sayayya a wata kasuwa da ke garin Menaka da ke karkashin ikon 'yan tawaye har suka kashe soja guda.

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan ruwan sama mai yawa da kuma ke barna a kasar Saliyo bayan ambaliya da kuma zaftarewar laka da ta janyo asarar daruruwan rayuka a tsakiyar watan Agusta. Jaridar ta ce gidaje na dubbannen mazauna Freetown babban birnin kasar Saliyo suka rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ci gaba da samu a birnin. Ana kuma fargabar barkewar annobar cututtuka kamar kwalera da zazabin Typhoid.