1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta yi sabon shugaba

Gazali Abdou Tasawa AH/SB
July 28, 2023

A Jamhuriyar Nijar, Majalisar Ceton kasa ta CNSP ta sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, ta bayyana Janar Abdourahamane Tchiani a matsayin jagoran kasar.

https://p.dw.com/p/4UW5K
Jamhuriyar Nijar | Janar Abdourahamane Tchiani, sabon shugaban gwamnatin mulkin soja
Janar Abdourahamane Tchiani, sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Da  misalin karfe 12 na ranar wannan Juma'a ce Shugaban Majalisar ceton kasa ta sojojin ta CNSP, Janar Abdourahamane Tchiani ya gabatar da jawabinsa na farko a gidan talabijin na kasar ta Nijar ta RTN inda a cikin wani jawabi na kimanin mintoci 9 ya bayyana dalilansu na kifar da gwamnatin ta Shugaba Mohamed Bazoum. Batun tabarbarewar tsaro a kasar da yadda ya ce gwamnatin ta gaza shawo kanta na daga cikin manyan dalilan daukar matakin in jin Janar Tchiani wanda ya zargi tsohon shugaban kasar da aikata laifuka masu yawa a fannin harkokin tsaron.

Karin Bayani: Sojoji sun tabbatar da Juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Screenshot DW Sendung Niger
Janar Abdourahamane Tchiani, sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da Mohamed Bazoum hambararren shugaban kasaHoto: DW

Sabon shugaban majalisar ceton kasar ya kuma zargi tsohon shugaban kasar da kin hada kai da kasashe makobta wadanda muke da matsala daya. Tuni dai kungiyoyin kare hakin dan Adam da demokuradiyya suka soma bayyana abin da suke jira daga sabon shugaban hukumar mulkin soja.

A wata sanarwar sojojin da suka yi juyin mulkin suka fitar a yanzu sun bayyana cewa duk da kokarin da suke na ganin kura ta lufa an kauce wa zubar da jini, suna da labarin wasu daga cikin manbobin tsohuwar gwamnati sun samu maboya a wasu ofisoshin jakadancin wasu kasashe inda suke kitsa shirin na amfani da karfi don neman kwato mutanensu da ke tsare. lamarin da suka ce zai zama babban bala'i ag mutanen kasar da ba su ji ba su gani ba.