Sojojin Najeriya 12 za su fiskanci hukuncin kisa
September 16, 2014A ranar Litinin din nan ce kotun soji da ke zama a Abuja fadar gwamnatin Najeriya ta sami wasu sojoji 12 daga cikin 18 da ke yaƙi da mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar da laifin cin amanar ƙasa dama wasu laifuka.bayan wani yunƙuri na hallaka jagoransu.
Sojojin a ranar 14 ga watan Mayu na shekarar nan ta 2014 sun kai harbi ga Manjo Janar Ahmed Mohammed da ke jagorancin sabuwar rundina ta bakwai ta sojan Najeriya a Maiduguri.
A hukuncin da birgediya Janar Chukwuemeka Okonkwo da ke jagorantar zaman kotun da ke sauraron shari'ar ta soji ya sanar 12 daga cikin sojojin an same su da laifi biyar daga cikin su ba su da laifi ɗaya an yanke masa hukuncin daurin kwanaki 28 da aiki mai wahala. Dukkanin waanda ake zargin dai matasan sojoji sun musanta abin da aka zargesu da aikatawa kuma mafi akasarinsu matasa ne.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourrahmane Hassane