1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Sojoji sun kira taro

Ramatu Garba Baba
December 27, 2021

Masu rike da madafun ikon kasar Mali sun soma wani taro da zummar mayar da kasar kan turbar mulkin demokradiya, amma kungiyoyin farar hula sun kauracewa taron.

https://p.dw.com/p/44sj9
Mali | Übergangspräsident Oberst Assimi GOÏTA
Hoto: Präsidentschaft von Mali

Kanar Assimi Goita da ya jagoranci juyin mulki a Mali, ya ce, taron zai yi nazari kan halin da kasar ta tsinci kanta dama darussan da ta koya daga rigingimun da suka biyo bayan juyin mulkin da kasar ta fuskanta sau biyu a cikin shekarar 2021 mai shirin karewa.

Kungiyoyi farar hula da masu rajin kare hakkin dan adam, sun ki amsa goron gayyatar da aka mika musu inda suka yi fatali da makassudin taron. Sojojin da suka kwace mulki a Mali na shan matsi daga Faransa dama kasashen yankin yammancin Afrika, na son ganin, sun mayar da ragamar mulki a hannun farar hula.

Kanal Goita da ke jan ragamar mulkin kasar, ya sha alwashin ganin an gudanar da zabe kamar yadda aka tsara, amma ya ce, matsalar tsaro na haifar da tarnaki ga zaben da aka shirya gudanarwa a watan Febrairun 2022 mai zuwa.