MINUSCA: Gabon ta fasa janye sojojinta daga rundunar
July 5, 2018Da farko Gabon ta yi dauki matakin janye sojojinta ne, bayan da a ka zargesu da laifuka na cin zarafin jama'a dama yi wa mata fyade a yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta MINUSCA.
Shugaban jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera da kuma sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ne suka lallashi Gabon kan ta sauya matakin janye sojojin 444 daga rundunar wanzar da zaman lafiyan da ke kokarin tabbatar da tsaron kasar mai fama da tashe-tashen hankula. Kawo yanzu dai ba a iya tantance laifukan da ake zargin sojojin Gabon da aikatawa ba.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta shafe tsawon lokaci ta na fama da tashin hankali da ke da nasaba da siyasa da kuma addini musamman ma dai a tsakanin mayakan Seleka da 'yan Antibalaka.