1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Dakarun Afghanistan karbe iko da iyaka da Pakistan

Suleiman Babayo LMJ
July 16, 2021

Dakarun gwamnatin Afghasnitan da matakan da ke tallama musu sun sake kwace yankin iyaka da Pakistan daga hannun tsagerun 'yan kungiyar Taliban masu dauke da makamai.

https://p.dw.com/p/3wa0g
Afghanistan Provinz Bamiyan | Kampf Sicherheitslräfte und Milizen gegen die Taliban
Hoto: Ashaq Akramy/DW

Dakarun gwamnatin Afghanistan sun kwace yankin iyakar kasar mai muhimmancin da kasar Pakistan daga hannun tsagerun kungiyar Taliban masu dauke da makamai. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito halaka mai daukan hoton kamfanin a yankin.

Mako guda da ya gabata 'yan Taliban suka kwace yankin iyakar. Shaidun gani da ido daga bangaren Pakistan sun bayyana irin dauki ba dadin da aka tafka tsakainin bangaren biyu gabanin samun nasarar dakarun gwamnatin Afghansitan na sake kwace yankin mai tasiri.

Tun lokacin da aka bayyana kudirin janye dakarun kasashen duniya daga kasar ta Afghanistan bayan shafe kimanin shekaru 20, 'yan Taliban suke amfani da damar wajen sake kwace yankuna da dama daga dakarun gwamnati.